A cewar Masrawy, cibiyar kula da kur'ani ta kasar Masar da ta sanar da gudanar da wani shiri na musamman na karatun watan Ramadan na shekara ta 1446, wanda ya hada da karatuttukan da za a watsa a karon farko.
Shirye-shiryen da wannan tashar kur’ani ta ke yi a cikin watan Ramadan, sun hada da kyawawan karatuttukan da manyan malamai suka yi, wadanda ake yadawa a karon farko.
Haka nan kuma za a rika gabatar da karatuttukan da ba kasafai ba na Sheikh Muhammad Rifaat kafin kiran sallar safe da yamma. Wannan tasha ce ta ke watsa shirye-shiryen karatun Al-Qur'ani na kusan awa daya daga bakin Sheikh Ragheb Mustafa Ghloush, Sheikh Shaaban Mahmoud Al-Sayyad, da Sheikh Muhammad Mahmoud Al-Tablawi.
Haka nan kuma gidan rediyon kur’ani na kasar Masar yana gabatar da cikakken Juz’i a kowace rana da karfe 10 na dare tare da sautin fitattun makarantun kasar Masar, wadanda suka hada da Sheikh Abdul Baset Abdul Samad, Sheikh Mahmoud Ali Al-Banna, Sheikh Muhammad Siddiq Al-Minshawi, Sheikh Mustafa Ismail, Sheikh Mahmoud Khalil Al-Hassari, Sheikh Muhammad Al-Hassari da sauransu.
Shirin karatun tafsirin watan Ramadan kamar haka.
A cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan, wannan kafar sadarwa tana watsa karatuttukan fitattun malamai na kasar Masar wadanda suka hada da Sheikh Abdul Baset Abdul Samad, Sheikh Mahmoud Ali Al-Banna, Sheikh Muhammad Siddiq Al-Minshawi, Sheikh Mustafa Mustafa Ismail, Sheikh Mahmoud Khalil Al-Hosari, a tsawon dare da rana, ta yadda za a rika watsa karatun kur'ani baki daya a cikin sautin wadannan mahardata daga karshen suratu.
Haka nan kuma ana watsa cikakken karatun kur’ani mai tsarki duk bayan kwana biyu, sannan ana bayar da bayani kan lafuzzan ayoyin a yayin karatun.
Tashar kur'ani ta kasar Masar tana gabatar da karatun kur'ani baki daya ta hanyar sautin fitattun malaman kasar Masar da suka hada da Sheikh Ragheb Mustafa Ghalouh, da Sheikh Shaaban Al-Sayyad, da Sheikh Muhammad Mahmoud Al-Tablawi, inda ake watsa karatun wadannan malamai uku bi da bi kafin a fara kiran sallar asuba.